14 Maris 2020 - 05:57
An Samu Bullar Cutar Coranavirus A Kasashen Ghana Da Gabon

Gwamnatocin kasashen Gabon Da Ghana sun tabbatar da kamuwar wasu mutane a kasashensu da cutar nan ta Corona Virus a karon farko a jiya Alhamis.

(ABNA24.com) Gwamnatocin kasashen Gabon Da Ghana sun tabbatar da kamuwar wasu mutane a kasashensu da cutar nan ta Corona Virus a karon farko a jiya

Alhamis.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya ce kasashen sun zo na 9 da na 10 a jerin kasancen da cutar ta bulla a cikin kasashen Afirka. Wato bayan kasashen Najeriya, Senegal, Togo, Afirka ta Kudu, Burkina Faso da kuma DMC Congo.

A kasar Gabon dai wani matashi dan shekara 27 a duniya, wanda kuma ya dawo kasar daga kasar Faransa a ranar 8 ga watan Maris da muke ciki ne yake dauke da cutar.

A kasar Ghana kuma ma’aikatar kiwon lafiya c eta bada sanarwan gano cutar a jikin yan kasar guda biyu wadanda suka dawo daga kasar Norway da kuma Turkiyya.

Cutar corona dai, duk tare da shigowarta nahiyar Afirka bata yadu a cikin kasashen ba. Kuma bata zama annoba ga mutane a nahiyar ba.


/129